Banki dai ta hanyar wata cibiyarsa mai suna NIRSAL a takaice, zai tsayawa manoman ne don samun lamani daga bankuna da hakan zai sanya samun taki da iri da kuma injinan ban ruwa ga manoman rani da sauran kayan aiki.
Babban manajan shirin Aliyu Abdulhamid Abbati, yace aikinsu ne su dauki takardun manoma su kaiwa bankuna domin samar musu da bashin da suke bukata. Ya kuma kara da cewa Najeriya zata iya ciyar da kanta ba tare da an shigo da abinci ba daga kasashen waje.
Gwamnatin Najeriya dai ta zuwa Naira Biliyan Saba’in da Biyar ga shirin NIRSAL, don samun karfin jarin lamuntar manoman a bankuna.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5