Barrister Abubakar Saddiq Idris shugaban gamayyar lauyoyi masu fafutikan kare hakkin bin Adama yace sun kira 'yan jarida ne domin bayyanawa duniya matsayinsu akan shawarar da gwamnatin Bauchi ta yanke na korar kamfanin AIT daga harabarsa.
Yace kamfanin AIT nada rajista kuma doka ya bashi damar mallakar kasa.
Shi ma Al-Mustapha Alhaji Shehu shugaban kungiyar masu sauraren labarai reshen jihar Bauchi yace su suna karuwa da kamfanin saboda haka hakkinsu ne su tashi su samo msalaha tsakanin kamfanin da gwamnatin jihar. Yace mutanen dake aiki a kamfanin kashi taca'in 'yan jihar Bauchi ne.
Kwamred S. Jibrin sakataren New Nigeria Peoples Party ko NNPP, reshen Bauchi yace kudurin gwamnatin ya hsafesu kai tsaye. Yace su da suke jam'iyyar adawa da sauran mutane da basu da ra'ayin gwamnati su ne za'a hana kafar bayyana ra'ayoyinsu, wato fadin albarkaccin bakinsu.
Muryar Amurka ta tuntubi Kwamred Sabo Muhammad babban jami'in dake ba gwamnan jihar Bauchi shawara kan lamarin. Yace dangane da kiranye-kiranye da ake yi tare da kiran da 'yan jarida suka yi gwamnan jihar zi yi masu adalci cikin abun da doka ta tanada.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da kaerin bayani.