Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Illar Da Tsagerun Avengers Suka Yiwa Tattalin Arzikin Najeriya


A wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ta ce Najeriya ta yi asarar Naira Tiriliyon 1.1 daga illar da tsagerun Niger Delta Avengers suka haddasa a wajen hakkar fetur cikin wata biyar da suka wuce.

A tsarin hakkar fetur ganga Miliyan Biyu da Dubu Dari Biyu a wuni ya ragu da kusan kashi Biyu cikin Uku. Masana na ci gaba da muhawara kan gibin da hakkan zai haddasa ga kasafin kudin Najeriya na bana.

Masanin tattalin arziki a birnin Abuja Usha’u Aliyu, yace “wannan yanayi na gibi ya hadu da gibin da dama kasafin kudin yake da shi, kaga yana da wahala a samu aiki da kasafin kudin Dari bisa Dari, kuma ba mai yiwuwa bane kawai.”

Kwararru dai na ganin abin da yakamata gwamnatin Najeriya ta yi yanzu shine a hanzar ta samun zaman lafiya da tsagerun na Niger Delta.

Hare haren Avengers dai na nuna bangaranci ne da ya sabawa ka’idar dimokaradiyya, wannan dai ra’ayin shugaban kungiyar yaki da cin hanci da wanzar da zaman lafiya Injiniya Ahmed Zakari Guroje.

Labarai da ga gonaki na nuna sabuwar Masara ta fara fitowa da ta rage tashin farashi da hakan ke nuna za a samu sauki daga radadin tattalin arziki ta wannan bangaren.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga birnin Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG