Babban bankin Najeriya (CBN) ya bada sanarwar sake tunasar da jama’a musamman ‘yan kasuwa akan dokar nan ta hana dukunkune takardar kudi, inda ya bayyana cewa dokar na nan daram kuma karya wannan doka na iya kai mutum ga gidan kaso.
Mataimakin daraktan babban bankin Najeriya, Benedict Maduagwu, ne ya bada sanarwar hakan a wani taro karawa juna sani na matasa maza da mata ‘yan kasuwa a da aka gudanar a jihar Akure.
Taron ya ja hankalin matasa akan yadda zasu rike takardar kudi da mutumci ba tare da dukunkune ta ba kamar yadda wasu kan yi.
A cikin gargadin, ya bayyana cewa kada a cukwikwiye takardar kudi, kada a yi rubutu akai, domin gwamnatin tarayya na amfani da kudin haraji wajan biyan kamfanin dake buga kudi, idan aka ci gaba da bata takardar kudi, bankin ‘yan kasuwa bazai sami isassun kudin da zai ba ‘yan kasuwa rance domin bunkasa harkokin kasuwanci.