Shahararren dan wasan damben Boxing Anthony Joshua, ya bayyana yadda yake matukar kaunar ganin shahararren dan wasan damben nan dake rike da kanbun damben boxing na duniya Wilder, ya amince da goron gayyata domin a tantace waye babban zakaran damben duniya a tsakanin su.
Joshua, ya bayyana cewa zai so ya Wilder, ya karbi wannan goron gayyata domin su fafata a filin wasa na Wembley, a ranar 13, ga watan Afilu, na shekarar 2019, a gaban ‘yan kallo 100,000.
Ana sa ran za a sami kudi wuri na gugar wuri dala Milioyan dubu dari, ($100,000), kuma shine na farko da zakarun ‘yan wasan damben Boxing hudu na duniya zasu hadu a lokaci guda.
Ya kara da cewa “fafatawa ta da Wilder ce mafi armashi ba Povetkin ba, domin idan aka ce an fasa wannan wasa lallai bazan ji dadi ba”
Ana sa ran za a wadannan zakaru za su fafata ne shekara mai zuwa domin tantance zakara a tsakanin manya manyan zakarun ‘yan damben duniya da suka yi fice.
Facebook Forum