A jiya Laraba wasu taron masana kimiyya suka ayyanar cewar, sun ga wani danshi da yake nuna alamun ruwa a karkashin duniyar Mars, wanda hakan ke kara tabbatar da cewar mutane zasu iya rayuwa a duniyar.
Matattarar ruwan nada fadin kimanin murabba’in kilomita 20, cikin dusar kankara, wadda wata na’ura da aka kaddamar a shekarar 2003 ta iya hasko tsibirin.
Masanann sun hango alamar cewar ruwa ya taba kwanciya a duniyar ta Mars. Hakan kuma yana nuna cewar mutane sun taba zuwa wajen, a cewar Farfesa Robert Orosei, na tsangayar binciken sararin samaniya na kasar Italiya.
Farfesan wanda ke jagorantar wannan binciken, kuma ya tabbatar da cewar akwai tabbatacin cewar ruwa na kwance a cikin duniyar wadanda har ya zuwa yanzu ba’a iya gano suba.
Ya kara da cewar fadin inda ruwan yake kwance ya kara tabbatar da cewar za’a iya rayuwa a duniyar, ba kamar yadda kankara take narkewa a cikin dutse ba.
Facebook Forum