Duba da ganin cewar ana dab da gudanar da zabe matasa a shirye suke domin sauya yadda ake tafiyar da mulkin demokradiya a Najeriya.
Ya ce matasa da suke zaune iyayen gidansu na kama hannunsu ba tare da sun cancanta ba sun dare karagar mulki, babu shakka wannan lamari zai sauya salo, domin kuwa a yanzu matasa sun sha alwashin sai sun taka rawa a cikin al’ummarsu kafin a mara masu baya a harkokin siyasa.
Ya kara da cewa a yanzu matasa sun farga don wani ya zo da kudi ya zo neman madafan mulki ba zai samu goyon bayan matasa ba, domin kuwa baya ga ilimi da suke bukata sai an duba cancanta da dacewarsa sannan ne matashin zai samu nasarar da yake tunanin kawo canji ga al’ummarsa.
Tata ya ce babu tantama matasa na fama da matsalolin shan kwaya da rashin alkibila hakan ne ya sa suka tashi suke tara matasa domin wayar masu da kai akan muhimmancin canji bangar siyisa da son kai da iyayen gidansu ke yi masu wajen basu kwayoyi su sha domin cimma wata manufa ta su ta son zuciya da sauya masu tunani.
Abubakar ya ce a zaben 2019, matasa sun tsaya cak suna kallon juyin juya hali domin ganin ko alkwarruan da aka yi masu an cika ko akasin haka kafin matasa su sake zaben wasu mutanen da zasu wakilce su.
Facebook Forum