Bankin CBN Ya Karyata Labarin Cewa Ya Umurci Bankuna Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Takardun Kudin Naira 500 Da 1000

Naira

Babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata labarin cewa ya umarci bankuna a kasar da su fara karbar takardun kudi na Naira dari biyar da Naira dubu daya.

ABUJA, NIGERIA - 'Yan sa'o'i bayan da wata sanarwar da aka ce daga Babban Bankin na (CBN) ta fito, cewa bankin ya bada wannan umarni ne, duba da halin matsatsi da jama'a ke shiga dangane da wannan manufa ta sauya fasalin Naira, sai gashi kuma wata sanarwa daga Babban Bankin na karyata ta farkon.

Sabbin kudin Naira

A sanarwa ta farko, wadda yanzu aka karyata, an ce babban bankin ya ce ya gindaya wa bankunan sharadin cewa kada mutum daya ya aje sama da Naira dubu dari biyar a lokaci guda, inda kuma ya ke jaddada cewa hakan ba ya na nufin amfanin takardun kudin na Naira dari biyar da Naira dubun bai kare ba.

Sanarwar ta farko ta ce babban bankin ya bada umarnin ne saboda yadda mutane ke ta fama a ofisoshin babban bankin dake jihohi.

Sabbin kudin Naira

Sanarwar ta farko, wadda aka karyata, ta ce za a iya aje kudin da amfaninsu ya kare ne bayan an ciccike takardu ta yanar gizo sannan a tafi bankin da wadannan takardun da aka cike ta yanar gizo da babban bankin Najeriya ya umarci bankuna su fara karbar takardun aje kudin.

Rahotanni daga sassan Najeriya daban-daban na nuna yadda batun sauya fasalin kudin ya fusata ‘yan kasar da ta kai ga sun fara bore, wanda hakan ya yi sanadin cinna wa wasu bankuna wuta da asarar rayuka.

Masana tsaro na fargabar wannan kunci da ‘yan Najeriya suka sami kansu a ciki ka iya jawo tarzomar da ka iya sa kome ya tsaya cik a kasar, muddin mahukunta ba su yi abin da ya dace a kan lokaci ba.