Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabinsa ne da bayyana cewa ya zama dole ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi a yau 16 ga watan Fabrairu kan halin da al’umma ke ciki da kuma yin tsokaci kan kokarin da gwamnatinsa ke yi na karfafa tattalin arziki mai dorewa, inganta yaki da cin hanci da rashawa da kuma ci gaba da samun nasarori a yakin da ake da ta’addanci da rashin tsaro, wanda babu shakka abubuwa da dama a ciki da wajen kasar sun yi tasiri a cewarsa.
Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin bukatar maido da ikon da babban bankin CBN ke da shi don ci gaba da ganin kudi na zagayawa yadda ba zasu saba wa doka ba.
A cewar shugaba Buhari, yana da masaniya a kan irin cikas din da wasu jami’an bankuna suke haddasawa wajen aiwatar da manufar rarraba sabbin takardun kudi a kasar, wadanda su aka dora wa alhakin aiwatar da sabon tsarin kuma lamarin ya bakanta masa rai kwarai da gaske, ya na mai cewa gwamnati bata da niyyar kuntata wa talakawa.
Shugaba Buhari ya ce bayan tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar domin kawo sauki a yanayin matsatsi da ‘yan kasa ke ciki, ya amince bankin CBN ya sake fitar da tsofaffin takardun kudi na naira 200 kuma a barsu su rinka yawo a matsayin takardar kudi mai amfani, da sabbin takardun naira 200, 500, da 1,000 har tsawon kwanaki 60 daga ranar 10 ga watan Fabrairu zuwa 10 ga watan Afrilu na shekarar 2023, lokacin da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 200.
Kazalika shugaba Buhari yace ‘yan kasa zasu iya kai tsofaffin takardun naira 500 da 1,000 zuwa ofisoshin bankin CBN a jihohi don karbar sabbi kamar yadda sashe na 20 sakin sashe na 3 na dokar CBN ta shekarar 2007 ya tanadar.
Daga karshe shugaba Buhari ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin nazari a kan yadda ake aiwatar da aikin manufar kudi da nufin tabbatar da cewa ‘yan kasar ba su cutu ba.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda hukunci kotun koli a kan lamarin zai kasance.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: