Ba'a Taba Yin Dan Takaran da Baya Nazari Kafin Yayi Kalamu Ba Irin Donald Trump-Dazan

Hukumar Zaben Najeriya

Yayinda yake magana a madadin hukumar zaben Najeriya akan zaben Amurka Nick Dazan kakakin hukumar yace tunda ya taso yana bibiyan harkokin zaben Amurka ba'a taba yin dan takarar shugaban kasa ba wanda baya nazarin kalamun dake fitowa daga bakinsa

Inji Nick Dazan abun takaici ne a ce jama'iyya irin Republican bata samu wani dan takaran da zai tsaya mata ba sai Donald Trump wanda kalamunsa na harzuka jama'a ne.

Yace jam'iyyar Republican ce ta samar da shuganni irin su Fraklin D Rosevelt, Ronald Reagan da su Bush da suka shugabanci kasar tare da yin gagarumin aiki da kawo cigaban kasar. Duk wadannan natsatsun mutane ne amma sai gashi an wayi gari an samu wani wanda zai sawa dimokradiya illa.

Yace kodayake a Najeriya dimokradiya jaririya ce koyo kuma su keyi amma idan sun ga abun da ba daidai ba dole su kauce masa. Su ba zasu yi koyi da abubuwan da Donald Trump ya keyi ba ta wajen kalamai da nuna kyama ga wasu da ingiza mutane har da ma tsoratar da mutane.

Nick Dazan yace duk wani mutum da zai sa mutane cikin zullumi bai kamata a ce shi ne ma zai yi shugabanci ba. Donald Trump ya baudewa siyasar akida ya kawo wasu abubuwa daban. Abun da yakamata shugaba ya damu dasu su ne yadda za'a yi zamantakewa da yadda za'a inganta rayuwar jama'a da yadda za'a yi zaman lumana.

Irin Trump bai kamata ya rike iko da karfin da Amurka ke dashi ba saboda zai yiwa kananan kasashe barazana.

Ga firar Nasiru El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba'a Taba Yin Dan Takarar da Baya Nazari Kafin Yayi Kalamu Ba Irin Donald Trump - Dazan -6' 31"