Yace ba a tado da wannan batu ba sai da ya rage sati daya kafin a jefa kuriar shugaban kasa.
Yanzu haka dai ‘yan jam’iyyar Democrat masu goyon bayan ‘yar takarar tasu, har ma da wasu ‘yan jam’iyyar Republican sun nuna fushin su akan sai yanzu ne Comey ya sake tado da wannan batu ana saura kwanaki 11 a jefa kuri’ar shugaban kasa, kuma sai gashi yana cewa wai bai sani ba ko sabbin wadannan Email dinsuna da nasaba da wadanncan da aka binciketa akansu ba.
Sai dai galibi hukumar ta FBI din bata bayyana lokacin da zata gudanar da bincikenta ba, musammam koda ko ba lokacin zabe bane.
Sai dai kuma Comey yace ya fada wa shugabannin majalisa cewa an kammala wannan binciken amma kuma yake jin ya zame masa wajibi cewa ya sake fada musu cewazai sake farrfado da wannan batu.
A sailin da shugaba Obama yake tattaunawa da wata kafar yada labarai ta yanar gizo wadda aka wallafa jiya Laraba, yayi gugar zana yana cewa an yikokarin a nuna cewa kamar baya da hannu cikin wannan badakalar na Hillary Clinton wanda ke kokarin neman kawo mata kafar ungulu tsakanin karawar da suke yi, ita da Donald Trump.