A zantawar da yayi da Muryar Amurka akan zaben kasar Dr. Aminu Gamawa yace sanarwar da shugaban FBI James Comey yayi akan email din Hillary Clinton makon jiya kamar yayi mata illa sosai.
Bayani da hukumar tayi na cewa har yanzu akwai saurar magana ya sa jikin magoya bayanta ya mutu yayinda masu goyon bayan Trump kuma suka samu karfafawa.
Amma tunda ba'a yi zaben ba Dr Gamawa yace babu mamaki wannan sabuwar sanarwar ta shugaban FBI James Comey ta karfafa magoya bayan ita Hillary Clinton. Yace dama wasu masu goyon bayanta 'yan Bernie Sanders ne mutumin da ya fafata da Hillary Clinton akan zaben fidda gwani. Duk lokacin da suka ji akwai wani abun shakka game da ita sai su ja baya. Yanzu da FBI tace ba zata tuhumeta ba zasu koma su goya mata baya.
A cewar Dr Gamawa sanarwar ta FBI labari mai kyau ne ga Hillary Clinton to saidai babu tabbas ko sanarwar zata sa Trump yayi hasarar wasu kuri'u ranar zabe. Duk da haka wankewar da FBI ta yiwa Hillary Clinton zai taimaketa har ma bayan taci zaben.
Ga firar da Dr Gamawa yayi da Muryar Amurka da karin bayani.