Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Republican Na Cikin Hadari - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama yayinda yake yiwa Clinton kamfen ajihar North Carolina
Shugaban Amurka Barack Obama yayinda yake yiwa Clinton kamfen ajihar North Carolina

Shugaba Barrack Obama yace yayi imani jamiyyar Republican na cikin hatsari muddin aka ce Donald Trump ne yaci zaben da za ayi a cikin satin nan mai zuwa.

Shugaba Obama yana magana ne a wajen kamfe da yake yiwa ‘yar takarar jamiyyar Democrat Hillary Clinton a Jihar North Carolina wadda take jiha ce da take da dimbin tasiri ga ‘yan takara, domin ko tilas neko wane dan takarar dake son shiga fadar White House to wajibi ne yayi nasara a wannan jihar.

Shugaba Obama yaci gaba da cewa bai jin cewa Amurka na cikin hatsari da ace ya fadi zabe lokacin da ya kara da John Mccain a shekarar 2008 ko kuma Mit Romny a shekarar 2012.

A dai dai nan ne yake gargadin masu jefa kuri’a na jihar ta North Corolina da cewa kar su dauka cewa kuri’ar ko wane mutum guda bata da tasiri. Yace sam wannan zaben ya wuce da haka, don haka kar su shantake gida suki zuwa jefa kuria domin yin hakan wata babbar illa ce ga wakilcinsu.

Shugaban yana magana ne musammam ga masu jefa kuri’a bakaken fata, wadandabasu nuna sha’awarsu ba domin kurun shi Obama baya takara wannan karon.

Sai dai kuri’ar baya-bayan nan a jihar ta North Carolina ta nuna cewa Trump na gaban Hillary da ‘yar tazara kadan wanda bai taka kara ya karya ba.

Shiko Trump a lokacin da yake yakin neman zabensa a jihar Florida yace zaben Clinton zai haifar da mummunar matsala ga dokar kasa wanda za’a dade ba a shawo kansa ba. Yace yadda ta sarrafa Email lokacin da take sakatariyar harkokin wajen kasar zai jefa ta cikin bincike koda ko tana shugabanci.

Shugaba Donald Trump ya ba gwamnatinsa damar tasa keyar bakin haure daga kasar, da kai wasu kurkuku na Guantanamo Bay dake Cuba
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Shehu Kanam mai sharhi kan al’amura ya mana karin bayanin matsayin dalilan yawaitar fashewar tankokin man fetur a Najeriya
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karin haske akan dalilan dake kawo aukuwar haduran tankar mai a Najeriya da musabbabin karuwar wannan lamari a baya-bayan nan
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG