Saidai kotun tsarin mulkin kasar ta takawa wannan yunkuri nasa burki.
A jawabin daya gabatar ta kafar talabijin kai tsaye ga al’ummar Senegal a jiya Alhamis 22 ga watan Fabrairun da muke ciki, Macky Sall yace:
“Kasancewar an rantsar dani a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 2019, ranar 2 ga Afrilu me zuwa wa’adin mulkin shekaru 5 zai kammala, kuma hakan zai kawo karshen wa’adin mulkina. Haka kuma, na kudirin aniyar dakata haka. Bayan 2 ga watan Afrilu me zuwa zan sauka daga matsayina na Shugaban Kasa.”
Bayanin na sa na zuwa ne bayan da kawancen jam’iyyun dake mulki ya amince ya tsawaita masa wa’adin mulkin a farkon watan Fabrairun da muke ciki.
A sa’ilin ne, wasu ‘yan majalisa daga bangaren adawa suka fice daga zaman Majalisar Dokokin kasar bayan da ta amince a sauya lokacin gudanar da zaben zuwa watan Disamba.
Bangarorin adawar dai na ci gaba da yin matsin lamba ga Shugaba Sall, wanda yace a shirye yake ya shiga tattaunawa a mako me kamawa.
“Babu yadda za’a yi kasar nan ta kasance ba tare da Shugaba ba. Tabbas tattaunawar da zamu yi za ta tsayar da matsaya, koma a cimma maslaha akan samun mafita. Ina fatan ‘yan siyasar dake kewaye da ni za su yi la’akari da makomar kasarmu. Zan saurari abinda zai fito daga tattaunawar, kuma bayan hakan, kotun tsarin mulkin kasa zata yi mana fashin baki game da batutuwan.”
Sha biyar daga cikin ‘yan takara ashirin din da suka amince su fafata a zabubbukan da aka jinkirta sun cimma matsaya akan sai dai a gudanar da zaben kan nan da ranar 2 ga watan Afrilu me zuwa.