Ba Zamu Bari "Barayi" Su Tsaya Takara Ba - EFCC

EFCC

Mukaddashin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu ya goyi bayan kiran da aka yi na hana “barayi” su tsaya takara a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Ibrahim Magu ya bayyana haka ne a cikin hirarsa da Muryar Amurka yayin wani taro da aka gudanar a babban birnin Tarayya Abuja, a daidai lokacin da hukumar ta fitar da jadawalin zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara din.

Ya kara da cewa, barazana ga ransa ba zai sa ya yi kasa a guiwa ba, ko kuma hana shi gudanar da aikinsa. Ya kuma jaddada niyar hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa “ba sani, ba sabo.”

Taron da ya hada kan fararen hula, wanda ya sami halartar lauyoyi, yan jarida da kuma ‘yan gwaggwarmaya, ya yi kira ga hukumar EFCC ta hana ‘yan siyasa da suka wawuri dukiyar al’umma tsayawa takara domin tsabtace tsarin da kuma zama ishara ga na baya.

Tun farko, mahalarta taron sun yi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta cika alkawarin da tayi na yaki da cin hanci da rashawa, ba tare da nuna wariya ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya ya aiko daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar EFCC Zata Hana Masu tabo tsayawa takara-2:26"