Kotun daukaka kara data zauna a Lagos ta ce hukumar EFCC bata da hurumin tuhumar alakalan kotu da ke kan aikinsu da duk wani zargi sai sun bar aiki. Kotun ta yanke hukunci ne kan wata shari'a tsakanin alkalin babbar kotun tarayya Ganjuwa, da ya kalubalanci hukumar ta EFCC da hararar bangaren alkalai.
Sai dai kotun tace EFCC zata iya tuhumar alakalan da hukumar alkalai ta sallama daga aiki. EFCC kuwa ta tuni ta yi watsi ne da hukuncin. Ta kuma bayyana aniyarta ta daukaka kara zuwa kotun koli. Ta bayyana hakan ne a sanarwar da Kakakin EFCC Mr. Uwujeren ya fitar. Inda ya kara da cewa, kotun kawai tana neman kare alkalai ne da suka aikata laifuffuka.
Kwana kwanan nan shugaban hukumar EFCC ya lashi takobin ci gaba da yaki da barayin biro ko da zai rasa ransa. A cewarsa, "Ba sani, ba sabo. Ba ma gudun kowa. Duk wanda yayi kuruciyar bera to zamu kwato kudin da ya sace mu mayarwa gwamnati sannan kuma mu mika gaban kuliya manta sabo".
Imrana Adam mai sharhi akan lamuran yau da kullum yayi tsokaci kan hukuncin kotun da cewa, kowa ya san Najeriya, iya kudinka iya shari'ar da zaka samu. Ba ka shakkan zuwa gaban alkali domin ka san Naira miliyan kaza zata iya kwatoka. Ba wai zargi bane, a'a abu ne da ya faru. Yace, kwanan nan wani alkali yayi ritaya kuma ana zarginsa da karban Naira miliyan dari.
A ra'ayin Imrana Adam hukuncin kotun shirme ne kawai, idan ba za'a iya kama alkalin da aka sameshi da cin hanci ba, har sai ranar da hukumar dake kula da alkalai ta sallameshi daga aiki. Ya kara da cewwa, ai kuwa dole ne EFCC ta daukaka kara idan kuma bata yi ba, to ta kwari al'ummar kasa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum