Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC ta Bukaci Yan Najeriya su Bata Hadin Kai a Yaki da Rashawa


EFCC
EFCC

Shugaban hukumar EFFC mai yaki da laifukan cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya, Ibrahim Magu, ya yi kira ga yan Najeriya su bada hadin kai ga wannan yaki da rashawa domin tabbatar da ci gaba a cikin kasar.

Ibrahim Magu ya yi wannan kiran ne a lokacin da hukumarsa ta shirya wani maci na tuna ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya a birnin Abuja. Najeriya kamar sauran kasashe masu tasowa tana fama da matsalolin cin hanci da rashawa lamarin da ke yiwa ci gaban kasar tarnaki.

Shugaban na EFFC, hukumarsa tana samun nasara domin galibin yan Najeriya na fahimtar aikin hukumar sai dai yan kalilan. Yace hukumarsa ta kara ilmantar da al’ummar kasa a kan cewa matsalar rashawa tana shafan kowa haka zalika shawo kanta na bukatar hadin kan kowa.

A hirarsa da wakilin mu Umar Faruk Musa, shugaban EFCC ya yi masa bayani cewa jami’an gwanmati da aka zargesu da aikata laifin rashawa za a gabatar da su gaban kotu idan aka tabbatar da laifinsu. Sai dai yace hukumarsa tana zurfafa bincike kuma ta tattara shaida masu sahihanci don haka take dadewa wurin gudanar da bincike.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG