A kashi na biyu na hira da 'yan jarida, dan Boko Haram da aka kama yayi magana kan yadda suke samun makamai, da horaswa da rayuwa cikin daji
WASHINGTON, DC —
Wani matashi dan kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram yace rayuwar da suke yi a cikin daji, rayuwa ce mai wuya, ta yadda da kyar suke iya wanka balle ma wanki. Ya ce ruwan sha ma da kyar suke samu.
Matashin yayi magana kan yadda ake kawo musu makamai a kan babura, da yadda ake nuna musu yadda ake warwarewa da hada bindigar, da kuma harba ta. Sannan yayi magana kan yadda suke samun kayan sarki na soja da suke sanyawa.
Haka kuma, ya tabo batun matan da aka ce 'yan kungiyar na kamawa, da yadda suke tafiya da makanikai in zasu kai hari domin sata ko kwace motoci.
Sannan kuma ya ce a yanzu soja da 'yan sanda ba su ne manyan abokan gabar 'ya'yan kungiyar dake warwatse ba.
Ga kashi na biyu na tattaunawar da Haruna Dauda yayi da shi.

Your browser doesn’t support HTML5