Ba Na Nadamar Matakin Janye Dakarunmu Daga Afghanistan - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden a lokacin da take jawabi ga Amurkawa kan rikicin Afghanistan

“Ci gaba da zaman dakarun Amurka a kasar na tsawon shekara daya ko shekara biyar ba zai sauya komai ba idan har sojojin Afghanistan ba za su iya rike kasarsu ba,” Biden ya fada a ranar Asabar cikin wata sanarawa.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba ya da-na-sanin matsayar da ya dauka ta janye dakarun kasarsa daga Afgahnistan.

Biden ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko da ya yi a baina jama’a tun bayan da Taliban ta samu cikakken ikon tafiyar da mulkin kasar wacce ke kudancin Asiya.

Yayin jawabin ga 'yan kasa, wanda ya yi ta kafar talabijin a ranar Litinin daga Fadar gwamnatin Amurka ta White House, Biden ya ce aikin da Amurka ta je yi a kasar “bai kamata a ce na gina kasa ba ne,” yana mai cewa matsalar barazanar ta’addanci da ta kai sojojin Amurka kasar ta fadada har zuwa wasu kasashe ba ma Afghanistan kadai ba.

Ashraf Ghani

Ya kuma bayyana cewa, nasarar da Taliban ta samu a kasar ta Afghanistan, “ta faru cikin dan kankanin lokacin da ba mu zata ba.”

Sai dai shugaban na Amurka ya ce kuskure ne a ce dakarun Amurka su ci gaba da yakin bayan su asalin sojojin kasar ba sa son yin fadan.

“Ko ba komai, abubuwan da suka faru cikin makon da ya gabata, sun kara min kwarin gwiwar,” matakin da Amurka ta dauka na janyewa daga Afghanistan ya yi daidai.

Biden ya koma Fadar ta White ne daga wajen shakatawa na Camp David, kwana guda bayan da Shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga Afghanistan a lokacin da mayakan Taliban suka kai ga isa Kabul babban birnin kasar.

Dakarun Amurka a Afghanistan

Shugaban na Amurka ya jima yana kare matsayar da ya dauka ta kammala shirin janye sojojin kasar nan da ranar 31 ga watan Agusta.

“Ci gaba da zaman dakarun Amurka a kasar na tsawon shekara daya ko shekara biyar ba zai sauya komai ba idan har sojojin Afghanistan ba za su iya rike kasarsu ba,” Biden ya fada a ranar Asabar cikin wata sanarawa.

“Kasancewar Amurka a tsakiyar yakin basasar wata kasa, abu ne da ba zan lamunta da shi ba.” Ya kara da cewa.

Dakarun Amurka sun kwashe shekara 20 suna kasar ta Afghanistan lamarin da ya gudana tsakanin gwamntocin shugabannin Amurka hudu.

A watan Afrilu Biden ya ayyana cewa zai kwaso dukkan dakarun Amurka nan da zuwa karshen watan Agusta, inda ya yi watsi da shawarar da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayar, kan cewa a bar wasu sojoji kalilan a kasar.

A lokacin Biden ya bayyana cewa, ba shi da burin ya bar wa shugaba na biyar aikin kwaso sojojin kasar zuwa gida.

Biden yana magana da wasu kawayen tsaro na NATO

Tun a farkon watan Mayu, Taliban ta zafafa hare-harenta a Afghanistan a lokacin da dakarun Amurka da kawayenta na NATO suka fara janye ragowar sojojinsu daga kasar.

Wasu hare-hare da kungiyar ta yi ta kai wa, sun ba ta damar karbe ikon yankuna da dama cikin dan sama da mako guda, lamarin da ya kai ga rugujewar gwamnatin kasar.