A zahirance babu kanshin gaskia dan gane da maganar da ake cewar kasar Amurika ta ce bazata cigaba da horas da sojojin Najeriya ba, wani wakilin kasar Amurikar Mr. James Eswel ne ya karyata hakan a Najeriya. Shima Mr. Mike Omere shugaban cibiyar samar da bayanai akan ayyukan ta’addanci a Nageriya, ya karyata wannan maganar. Yace Nageriya bata fadi haka ba, dama horaswar an shirya tane wajen kashi uku wannda kuma har sunyi kashin farko da na biyu, yanzu dama ana maganar kashin karshene, sai gwamnatin Nageriya taga bai kamata ace tana fama da yaki da ta’addanci a wannan lokaci kuma ace ta dauki wasu kayan aiki don kaiwa ga wani wuri inda ake horo ba. Tsakanin Nageriya da Amurika akwai hanyoyi daban daban wanda suke tattaunawa dangane da har kar tsaro da dai sauransu.
Shi kuma wani me sharhi a kan harkar tsaro a Nageriya Al-mustapha Liman yace Nageriya yakamata ace ta dauki wasu mata kai gwarara ba lallai sai ta dogara da wasu kasashe ba, ya kuma kara da cewar, ai Nageriya ita ta gayyato Amurika, wanda kuma Amurika ta bayyana ma Nageriya a matsayinta na kasa masu kwararu a harkar tsaro da sauransu ga yadda yakamata a billoma abun wanda ya kamata ace Nageriya ba wai ta dogara ga Amurika kadai ba, ai a kwai sauran kawayen ta kamar su Rash, Faransa da dai sauransu. Kai koda ace ana yaki da kara ne to yakamata ace Nageriya tayi galaba a wannan matsalar, don idan har sojojin Nageriya zasu iya zuwa wasu kasashe don kwantar da tarzoma kuma suyi nasara to wanna ai bai kamata ace ya tsole ma sojojin Najeriya ido ba. Yace ai wanna yakin cikin gida da bai wuce jiha goma ba wanda yakamata ace sojojin Nageriya sun san ciki da wajen komai, don haka sai antashi tsaye kamin a yi nasara akan wannan matsalolin.
Your browser doesn’t support HTML5