Alhaji Sa'adu Bello jami'in hukumar bada agajin gaggawa dake kula da 'yan gudun hijirar dake Yola ya bayyana halin da mata ke ciki a sansanonin.
Kawo yanzu a cikin matan da suka yiwa rajista an samu 35 da suka haihu. Akwai kuma mata masu ciki su ashirin da daya a wani sansanin. Hukumar na basu taimako. Na daya ana tabbatar cewa an kai matan asibiti domin kada su haihu a cikin yanayin da suka samu kansu. Za'a tabbatar an yiwa jariran alluran rigakafi. Masu jegon za'a samar masu da kayan abinci na musamman. Ko bayan sun haihu ana cigaba da kula dasu da jariransu.
Akwai wasu ma da suka haihu akan gudunsu na yin hijira. Wata daga Madagali akan hanya ta haihu.
Dangane da wadanda suke makale a kasashen Niger da Kamaru Alhaji Bello yace an kafa kwamitoci biyu. Daya zai tafi Kamaru daya kuma zai nufi Niger domin zakulo wadanda suka makale can. Saida ko a makon jiya wasu su 20,000 sun dawo cikin kasar daga kasashen Kamaru da Niger.
Ga rahoto.