A firar da yayi da Muryar Amurka Alhaji Abdullahi Bego kakakin gwamnatin jihar Yobe ya bayyana cewa gwamnati ta kafa dokar hana fita a birnin Damaturu da dalilan da suka sa aka kafata.
Da farko dokar ta hana kowa fita gaba daya jiya Talata. Kowa an tilasta masa ya kasance cikin gidansa har na tsawon sa'o'i 24. To amma daga yau Laraba dokar zata fara aiki ne daga karfe shida na yamma har zuwa karfe bakwai na safe wanshekare. Dokar zata cigaba da aiki har sai an samu tabbacin babu wata barazana daga kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin ta ce tana aiki da jami'an tsaro kuma zasu dinga kula da lamarin da ake ciki. Idan nan gaba sun ga akwai dalilin sassauta dokar zasu yi hakan. Kawo yanzu dai babu ranar dakatar da dokar sai abun da hali yayi, wato sai shawarar da jami'an tsaro suka baiwa gwamnan.
Rahotanni sun nuna an samu nasara akan 'yan Boko Haram. Burinsu na cafke birnin Damaturu bai cimma ruwa ba, sabili da haka ana tababan hujjar kafa dokar. To amma kakakin gwamnatin yace rahotannin da suka samu sun nuna masu cewa akwai wasu 'yan Boko Haram da suka bazu cikin garin domin basu san garin ba. Sabili da haka dokar zata baiwa jami'an tsaro damar zakulo irin wadannan mutanen domin kada su sake haduwa su yi wata barna.
Inji Alhaji Abdullahi Bego sabili da kokarin jami'an tsaro da hadin kan jama'a abubuwa sun fara komawa yadda suke da. Kwanciyar hankali da zaman lafiya sun fara dawowa. Abubuwa sun lafa kwarai da gaske.
Ga karin bayani.