Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutane 10 Sun Mutu a Wukari


Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.
Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.

Rahotanni daga Jihar Taraba na cewa wani sabon tashin hankali mai nasaba da kabilancin addini ya sake barkewa a Gindin Dorawa a karamar hukumar Wukari.

A halin yanzu dai bayanai na nuna cewa an sami asarar rayuka da dukiya yayin da aka tura karin jami’an tsaro.

Wani mazaunin garin Wukari wanda ya so a sakaye sunanshi cewa yayi “walLahi mu kanmu baza mu san meke faruwa ba, saboda harbe-harbe ne suka fara jiya, daga cikin anguwannin Jukun, daga bisani kuma sai kone kone”.

“Akwai mutane goma sha, wadanda suka mutu”, mutum ya kamala.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Joseph Kuji, yace ana binciken wannan lamari.

Kuji yace “a take, an tura ‘yan sanda da mobilawa da sojoji, yanzu da muke magana, kura ya lafa.”

Korafin da jama’a keyi na cewa jami’an tsaro basu isa ba wadannan yankuna ba, yasa ASP Joseph Kuji ya mayar da martani.

“Wannan magana ne kawai, jami’an tsaro sun taka rawar gani a wannan abunda ya faru.”

Jama’ar Jihar Taraba sun kwana biyu suna ganin tashe-tashen hankula masu nasaba da kyamar al-ada ko addini ko kabila.

Sama Da Mutane 10 Sun Mutu a Wukari – 3’15”
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG