Yankunan da ke fama da matsalolin rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da zama cikin wannan yanayi kuma ko da an ga alamun samun sauki sai abin ya koma baya, kamar yadda ya faru a garin Ghandi a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya wanda ya sha fuskantar matsalolin rashin tsaro fiye da shekaru biyu.
Yanzu haka mutanen garin na juyayin rashin rayukka kimanin 20 wadanda aka rasa sanadiyar fafatawa da jama'a suka yi da barayi.
Wani malamin asibiti dake garin Ghandi wanda sune suka yi hidimar wadanda aka harba da aka kawo asibiti ya bayanna cewa matsalar ta soma ne daga kashe jagoran ‘yan sakai wanda barayi suka samu labarin cewa ya je gonar sa shi kadai suka kai masa farmaki.
Rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta bakin kakakin ta ASP Sanusi Abubakar ta tabbatar wa muryar Amurka da aukuwar lamarin.
Yankin gabashin na Sakkwato dai na cikin wuraren da matsalar rashin tsaro tayi kamari a arewacin Najeriya inda jama'ar yankin su ke ta kokawa akan lamarin.
Wadannan matsalolin suna faruwa ne duk da yake an samar da jami'an tsaro a yankunan, abinda yasa masu sharhi akan lamurran yau da kullum ke ganin cewa lalle ya kamata a sake lale.
Matsalar rashin tsaro dai a Najeriya taki ci ta ki cinyewa kuma duk da kokarin da ake yi abin ya tashi tamkar ba'a komai.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5