Auren Dole Zai Dauki Sabon Salo a Kano

Sarkin Kano Alhaji Mohammadu Sunusi Lamido.

Sarkin Kano Alhaji Mohammadu Sunusi Lamido, ya karbi bakuncin shugabannin hukumar kula da gyaran dokoki ta jihar Kano a fadar sa karkashin jagorancin mai shari’a Wada Umar Rano.

Sarkin yace matakin ya zama wajibi ta yadda auren dole ya dauki sabon salo a wanna zamani inda yace ayanzu wasu mutanene ke amfani da dukiya ko mukami ko kuma abin hannun su wajen jan hankalin makwadaitan iyaye domin aurar musu da ‘ya ‘ya.

Kuma a yayinda Sarkin Kano ke muradin samar da dokar dazata kawo karshen yanayin auren dole, shi kuwa Alhaji Mohammadu Ali Mashi dake zaman jami’in kungiyar dake fafutukar bada kariya ga yara ‘kanana musamman ‘yan mata, shikuma yace, “ doka wadda naso ace a karfafa ayita, dokar da zata bawa yara kariya, kangiya daga dukkan cin zarafi wannan doka ta yara itace yakamata ace an karfafa.”

Wannan dai hukumace ta gyaran dokoki ko inganta dokoki ta jihar Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kano Kan Auren Dole - 3'25"