Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turai 'Yar'Addu'a Tayi Magana Akan Daliban Chibok


Hajiya Turai 'Yar'Addu'a.
Hajiya Turai 'Yar'Addu'a.

A cikin firar da tayi da abokiyar aiki yayain da ta kawo ziyara nan wurinmu, Turai 'Yar'Addu'a matar shugaban kasar Najeriya marigayi Alhaji Umaru 'Yar'Addu'a ta tabo batun 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.

Tace kowace uwa dole tayi juyayi da halin da 'yan matan suka shiga. Tace lamarin bashi da dadi sam. Tace a idan da diyarta aka sace yaya zata yi.

A akasarin gaskiya kowace uwa tayi juyayi kuma sun yi addu'a sun yi azumi akan 'yan matan. Sun roki 'yan kungiyar ta Boko Haram su yi kokari su sako yaran. Tace yaran babu ruwansu. Ilimi suka je nema domin rayuwar yau da kullum.

Idan fada ne kamata yayi 'yan kungiyar su je su yi fada da wadanda suke fada tare amma ba da yaran ba. Ko a addini idan ana yaki ba'a taba yaro. Saboda haka tace tana roko kuma tana kara rokon 'yan Boko Haram su sako yaran.

Tayi addu'ar Allah ya tabbatar da yunkurin sako yaran da aka ce gwamnatin tarayya nayi da kungiyar.

Akan ko abun da ya samu daliban ya gurgunta ilimin yankin tare da saka shakku cikin iyaye da daliban sai Turai tace tabbas lamarin ya shafi ilimi. Bugu da kari iyayen da ma suka gudu sun ki su sa yaransu makaranta sabili da tsoron abun da ka faru dasu.

To amma tace idan gwamnati zata iya sa tsaro ilimi zai farfado a yankin. Idan an tabbatar ma iyaye cewa babu abun da zai sami 'ya'yansu zasu yadda musamman idan sun ga an sa tankuan yaki domin kare makarantun. Dole gwamnatocin jiha da na tarayya su tabbatar cewa dalibai sun samu kariyar da ta dace a makarantunsu idan har ana son a farfado da ilimi. Tace ko ita ce ba zata yadda ta kai danta inda babu tsaro.

Ga firar da aka yi da Turai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

AGOGON CHIBOK:

Yawan lokacinda ya wuce tun daga ranar da aka sace ‘yan matan Chibok.

XS
SM
MD
LG