Aung San Suu Kyi Zata Kai Ziyarar Farko A Rohingya Bayan Hare Haren Da Sojoji Suka Kaiwa Musulmi

Aung San Suu Kyi

Shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi ta tafi jihar Rakhine ta arewa inda aka yi fama da tashin hankali, karon farko tunda rundunar soji ta kaddamar da hari kan Musulmin Rohingya tsirarru.

Kakakin Aung San Suu Kyi yace tana kan hanyar zuwa lardin Maungdaw dake kan iyaka daga Sittwe, babban birnin jihar Rakhine inda ta isa yau da safe.

Mayakan Rohingya sun kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda a Myanmar a watan Agusta, abinda ya sa sojoji suka kaddamar da hari a kauyukan Rohingya da ya haifar da kaurar mutane dubu dari shida daga Rakhine zuwa Bangladash, galibinsu suka yi tururuwa zuwa Cox’s Bazar. Kimanin kashi sittin cikin dari na ‘yan gudun hijiran kananan yara ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyan harin da aka kaiwa Musulmin Rohongya a matsayin kisan kare dangi.