Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar Na Gani Akwai Dalilin Da Ya Sa Bangladesh Ke Jinkirta Maida 'Yan Rohingya Kasarsu


Kudin agajin jinkai da Bangladesh ta samu daga kasashe na iya kawo tsaiko a shirin maida 'yan Rohingya kasarsu a cewar gwamnatin Myanmar.

Kasar Myanmar na zargin kasar Bangladesh da jinkirta maida musulmin Rohingya kasarsu, bayan da aka tilasta masu barin kasar don kaucewa mummunan farmakin da sojojin kasar ta Myanmar suka yi masu.

Wani mai magana da yawun daya daga cikin shugabannin Myanmar Aung San Suu Kyi, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Global New Light mallakar gwamnatin kasar yau Laraba cewa, Bangladesh na jira ta fara shirin maida ‘yan gudun hijirar sai kuma ta sami agajin dala miliyan 400 daga kasashe da suka bada gudunmuwa don fadada matsugunnan da aka warewa ‘yan Rohingya su 600,000 dake zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira da suka cika makil da jama’a.

Mr. Zaw Htay, ya kuma ce yanzu muna tsoron kada Bangladesh ta jinkirta shirin maida ‘yan gudun hijirar bayan da ta karbi wadannan kudaden.

Ya kara da cewa Myanmar na jira ta karbi sunayen ‘yan Rohingya dake Bangladesh a hukumance. Ya kuma ce kasar ta amince ta karbi ‘yan Rohingya muddun suka nuna cewa sun taba zama Myanmar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG