Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Amurka Ta Ce A Gaggauta Kai Dauki Ma Al'ummar Rohingya


Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, na shan suka daga kasashen duniya
Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, na shan suka daga kasashen duniya

Watakila gurnanin Amurka zai sa kasar Myanmar ta fara tunanin daina gallaza ma 'yan kabilar Rohingya tsiraru, wadanda daruruwansu su ka tsere zuwa kasar Bagladesh neman mafaka.

Tun ma kafin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yanke shawara kan ko ta'asar da sojojin Myanmar ke aikatawa kan 'yan Kabilar Rohingya masu rinjayen Musulmi, za a iya ayyana ta a matsayin kisan kare dange, 'yan Majalisun Dokokin Amurka sun shiga matsa ma gwamnatin kasar, cewa lallai ta magance wannan tashin hankalin.

Majalisar Dokokin ta Amurka ta yanke shawarar yin tir da wannan tashin hankalin, sannan ta yi kira ga Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi da ta fito karara ta la'anci wannan al'amarin.

Wannan matakin sharar fage ne na irin abin da Majalisar Dokokin za ta dauka, wanda daga baya zai hada da kakaba takunkumi kan bangaren sojin kasar. To amma 'yan Majalisar Dokoki irin su Sanata Richard Durbin na jam'iyyar Democrat, ya ce dole ne kasar Myanmar, wadda ake kuma kira Burma, ta dau matakin gyara yanzun nan.

Sanata Durbin da wasu takwarorin aikinsa na Republican da Democrat sun gana da Jakadan Myanmar a wannan satin, inda su ka gaya masa cewa dangantakar kasar tasa da Amurka fa ta ta'allaka ne kan yadda kasar tasa ta tinkari wannan tashin hankalin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG