Rundunar sojojin ruwan Amurka da Najeriya sun jagoranci atisayen Express Obangame, wanda ya hada da kasashen duniya fiye da 30 a Najeriya, wadanda galibinsu sun fito ne daga kasashen dake gabar tekun Guinea.
Vice Admiral Ebok Ibas, ya ce an gudanar da atisayen ne don karfafa hadin kai da aiki tare da musayar bayanai da kuma hana duk wani nau’in ta’addanci ta cikin ruwa.
Cikin manyan kasashen duniya da suka shiga wannan atisaye sun hada da Amurka da Faransa da Portugal.
A cewar laftanal kwamanda Abubakar Mai Gado, kasar Najeriya ce kadai rundunar sojojin ruwanta ke da jiragen sama a fadin nahiyar Afirka.
A ‘yan shekarun nan runudonin sojojin ruwan Amurka da Najeriya na ‘kara mayar da hankali sosai kan gabar tekun Guinea. Masanin tsaro kanal Aminu Isah Kwantagora, ya ce yankin tekun Guinea ya na da matukar muhimmanci kasancewar duk tattalin arzikin kasashen yankin suna bi ne ta wannan teku.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5