Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare 'Yancin Zabiya Ta Koka Kan Wariya Da Ake Nuna Wa 'yayanta.


Zabiya a Mali.
Zabiya a Mali.

Kungiyar ta shirya wani taron karawa wayarda kan jama'a cewa babu banbanci tsakanin su da sauran Bil'Adama.

Da yake magana bayan da ya halarci taron, babban alkali a kotun birnin trayyar Abuja, Mai Shari'a Usman Bello, ya bayyana takaicin jin yadda ake nunawa wadannan mutane wariya.

Yace irin wannan taro yana da muhaimmanci wajen kara wayarda kan al'uma kan bukatar su kara gyara halayen su ta wajen daina tsangwama da danne hakkin zabiyan a wuraren daukar aiki da sauran mu'amaloli.

Kungiyar tace akwai bukatar al'uma ta gane cewa babu wata illa don Allah ya baiwa mutum rabo na da ko diya zabiya, domin suma mutane ne kamar kowa.

Kungiyar ta kara da cewa suna fuskantar wariya,ind a har aka bada misali da wani zabiya, wanda yaje aikin horo na shiga aikin Dansanda, kuma ya nuna bajinta, amma daga bisani aka ki bashi takardar kama aiki.

Ga karin bayani a rahoton Saleh Shehu Ashaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG