Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Ingila Za Su Kece Raini a Wembley


'Yan wasan Najeriya suna gaisawa tare da shugaban Najeriya Super Eagle, a lokacin da kofin duniya ya isa birnin Abuja
'Yan wasan Najeriya suna gaisawa tare da shugaban Najeriya Super Eagle, a lokacin da kofin duniya ya isa birnin Abuja

Najeriya da Ingila za su fafata yau Asabar a wasan sada zumunci a matakin ta da tsimin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a wata nan na Yuni.

A yau Asabar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, za ta kara da tawagar ‘yan wasan Ingila, a wani mataki na ta da tsimin tunkarar gasar cin kofin duniya da za a fara a Rasha a wannan wata.

Za a yi karawar ce a fitaccen filin wasa nan na Wembley da ke birnin London, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Najeriya na rukunin “D” da ke dauke da Crotia, Argentina da Iceland a gasar cin kofin duniya.

A baya Najeriyar ta kara da Poland, Serbia, Congo, sai wannan karawa da za ta yi da Ingila kamar yadda jaridar Daily Post ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Najeriyar ta doke Poland da ci 1-0, ta sha kashi a hannun Serbia da ci 2-0 ta tashi kunnen doki da Congo inda aka tashi 1-1.

Sai dai yanzu haka, rahotannin sun bayyana cewa, tawagar ta Najeriya za ta samu nakasu, bayan da dan wasanta na gefe Moses Simon ya samu rauni a lokacin da suke atisaye.

Bayan Simon, akwai dan wasa Winfred Ndidi da shi ma ake kyautata zaton ba zai buga wasan ba a cewar shafin yanar gizon wasannin na ESPN.

Kuma tuni masu sharhi a fagen wasan kwallon kafa ke cewa mai yiwuwa ‘yan wasan ba za su samu damar taka leda a gasar cin kofin da za a yi a Rashan ba.

Bayan wannan karawa da Ingila, kungiyar ta Super Eagles za ta kara da Czech Republic, wanda shi ne wasan sada zumunci na karshe da za ta yi kafin danganawa da Rasha.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG