Arsenal Ta Shirya Saida Dan Wasanta Partey, Yayin Da Red Star Belgrade Ta Sanar Da Kulla Yarjejeniya Da Addo

Thomas Partey

Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta shirya sayar da dan wasan tsakiya Thomas Partey a lokacin buda kasuwar cefanen ‘yan wasa ta bazara, bisa sha’awa da wasu kungiyoyin Saudi Arabia suka nuna kan dan wasan.

Rahotanni na cewa Arsenal na tuntubar wakilan dan wasan na Ghana kan yadda wasu kungiyoyi za su nuna sha’awarsu, ko da yake a yanzu haka kungiyoyin Saudiyya kadai suka nuna sha’awa kan sa.

A gefe guda kuma, zakarun kwallon kafa na Red Star Belgrade a Serbia sun kammala kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiyar Ghana Edmund Addo.

'Yan wasan Ghana Black Stars

Dan wasan na Black Stars ya koma wurin zakarun Serbia ne a karkashin kwantaragin shekaru 4 daga abokiyar adawarsu ta Spartak Subotica, yayin da aka bude kasuwar 'yan wasa ta bazara.

Ana sa ran Addo zai taimaka wajen karfafa The Red And Whites gabanin kakar wasannin 2023/24, yayin da Red Stars ke shirin yin gumurzu a UEFA Champions League.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Arsenal Ta Shirya Saida Dan Wasanta Partey, Yayin Da Red Star Belgrade Ta Sanar Da Kulla Yarjejeniya Da Addo.mp3