Sabon shirin arewa a yau zai duba shawarwarin hanyoyin raya tattalin arzikin arewa ta hanyar kama sana’o’i, raya noma da kuma amfana da dimbin ma’adinai.
Masana na cewa akasarin ‘yan arewa na fassara azancin zancen kwanan kaza a kan dami.
A kan samu wasu matasa daga arewa na tafiya kurmi don yin ‘yan kananan sana’o’I kamar yankan farce wato kumba, lodin kaya a kamfanoni da ma tuka babur don sufurin achaba.
Matasa da kan yi gudun na duke tsohon ciniki kan ce rayuwar gararamba a birane ta fi mu su sauki da ratsawa cikin karangiya amma ai Bawan damuna baturen rani ne.
Injiniya Sa’ad Abubakar Abdullahi da ya ke matsayin tsohon ma’aikaci a kamfanin main a NNPC ya ce baya ga batun neman man fetur a arewa, kar a daina raya lamuran noma.
Shi ma tsohon dan bokon arewa Alhaji Yusuf Adamu ya kara karfafa bayanan Injiniya Sa’ad ne.
Saurari shirin a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5