Akwai kimanin yara miliyan 13 da ke ragaita kan titunan arewacin Najeriya, ko dai da sunan bara ko kuma iyayen su ba sa iya daukar nauyin su.
Dan majalisar dokoki Shehu Balarabe Kakale daga Sokoto, ya jagoranci tsarawa da samar da dokar da tsohon shugaban kasa Buhari ya sa mata hannu.
Shirin ya kuma dora daga inda ya tsaya a makon jiya inda mai kula da tura dalibai karatu zuwa kasashen Larabawa daga jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ya ci gaba da bayani kan bin kadin daliban da rikicin Sudan ya tilasta su ka dawo gida.
Saurari shirin cikin sauti: