Sabon shirin arewa a yau zai ci gaba da duba sanya hannu kan dokar kafa hukumar kula da almajirai da tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi a jajiberin sauka daga mulki sai kuma mu ji shawarar wani kwararren tsohon babban ma'aiakcin kamfanin NNPC kan yanda jihohin arewa da ke nesa da teku za su samu sauki daga dan karen tsadar man fetur.
Dan majalisar da ya jagoranci shirya dokar kafa hukumar kula da almajirai Dr.Balarabe Shehu Kakale na bayanin yanda hukumar za ta yi aiki wajen tallafa wa almajirai da ma yaran da ba sa samun kulawar da ta dace.
Karin farashin litar man fetur da ya bambanta daga jiha zuwa jiha ya fi tsanani a jihohin arewa da ke nesa da bakin teku. Tsohon babban ma'aikacin kamfanin man fetur na NNPC Injiniya Sa'ad Abdullahi Majidadi ya ba shawarar hanyar da za a iya samun sauki.
Saurari shirin: