AREWA A YAU: Abun Da Ya Dace a Yi Wa 'Yan Gudun Hijira Don Dawo Da Su Hayyacinsu - Yuni 28, 2023

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Shirin ya duba yanda ya dace a tallafawa dimbin 'yan gudun a yankunan da su ka fuskanci kalubalen tsaro a arewacin Najeriya kama daga arewa maso gabar zuwa arewa maso yamma.
Shirin ya duba abun da ya dace a yi wa 'yan gudun hijirar don dawo da su haiyacin su bayan maida su garuruwan su na asali.
Kazalika shirin ya duba muhimmancin aikin agaji na taimakon farko da wasu kungiyoyi ke samarwa kyauta da hakan ya zama daukin farko ga wadanda ke matukar bukatar taimakon gaggawa. Duk da aikin na sa kai ne amma ya na bukatar kwarewa da samun Katin shaidar gudanar da shi bisa dokokin kasa.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU: Abun Da Ya Dace A Yi Wa 'Yan Gudun Hijirar Don Dawo Da Su Haiyacin