Lauyoyin Shugaba Donald Trump na nazarin yiwuwar an aikata son zuciya a kwamitin bincike na musamman karkashin Robert Mueller, wanda za su kafa hujja da shi wajen yin watsi da sakamakon binciken Mueller game da katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Shugaban kasar Amurka, a cewar majiyoyi da dama.
Jaridar New York Times ta jiya Jumma'a ta ruwaito cewa hadiman Trump na binciken alakar siyasa da ta yau da kullum ta masu binciken don shirin abin da aka bayyana da 'arangamar da ke tafe' tsakanin Trump da Mueller.
An ce bangaren Trump na binciken komai, kama daga yadda masu binciken su ka yi ta bayar da gudunmowa ga 'yan takarar jam'iyya Democrat da kuma dangantakar Mueller da tsohon Shugaban FBI James Comey, wanda Trump ya kora.
Wani dan tawagar lauyoyin Trump na waje, Jay SEkulow, ya ce lauyoyin za su yi nazarin batun son zuciya su kuma gabatar da shi a lokacin da ya dace, ciki har da gabatar da korafi ga Mueller kai tsaye.