A wata sanarwa da shugaban kwamitin kamfe din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Honarable Chibuike Amechi dake zaman gwamnan jihar Rivers yanzu haka ya fidda, yace zasu dauki wannan matakin ne saboda Mrs. Dame Patience ta bada umurnin a jefi ‘yan jam’iyyar APC.
Yanzu haka dai akwai wani faifayin bidiyo dake yawo a yanar gizo na uwargidan shugaban kasa Dame Patience Jonathan, inda tayi kira ga magoya bayan su akan cewa duk wanda ya ce masu " Canji", su jefe shi. Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne a garin Calabar na jihar Cross Rivers a lokacin yakin neman zabe.
Gwamna Amechi ya cigaba da cewa wadannan kalamai na tunzura jama’a ne. sanarwar ta kuma ce irin wannan ikirari ne uwargidan tsohon shugaban kasar Kwadebuwa tayi, na kiraye-kiraye da suka tada hankali a gabanin zaben kasar na shekarar 2010.
Gwamna Amechi ya kuma ce tuni suka aike da wasika zuwa ga babban Speto-Janar din ‘yan sandan Najeriya, Suleiman Abba da kuma hukumar nan ta kare hakkin bil’adama domin daukar mataki. Gwamna Rotimi ya kara da cewa jam’iyyar su ta APC jam’iyya ce da ke kaunar zaman lafiya, don haka ba za su goyi bayan duk wani mai tada zaune tsaye ba. Mr. Rotimi Amechi ya kuma ce idan kana tare da Ubangiji, Ba abinda zai tsorata ka.
Da yake maida murtani, masanin shari’a Abdullahi Jalo, mataimakin kakakin jam’iyyar PDP ta kasa kuma, ya fadi cewa a irin wannan lokacin ba abinda ‘yan adawa ke yi illa su dauki bakin jini su yarfawa jam’iyyar PDP don a durkusar da ita. Ya kuma bayyana kalaman gwamna Amechi a matsayin shashi fadi.
Mohammed Ahmed Jamo, lauya mai zaman kansa a Najeriya yace tun da Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka sa hannu a kotun duniya, matukar wani dan kasar ya ga cewa an keta mai hakki, ko ya ga laifin yaki, ko na kisan kare dange. Zai iya gabatar da koken shi a ofishin kotun dake birnin Hague. Game da uwargidan shugaban kasa da ‘yan jam’iyyar adawa suke zargi da wannan laifi kuma, kamata yayi a ce hukumomin Najeriya sun gurfanar da ita gaban kotu amma ba a yi hakan ba - a ta bakin Mohammed Jamo.
Your browser doesn’t support HTML5