Sifeto Janaran 'yansandan Najeriya Suleiman Abba ya yiwa wadanda ya kira masu zuga kananan 'yansandansu su tayarwa manyansu kayar baya.
Suleiman Abba ya zargi wasu mutane da yace suna zuga kananan 'yansanda domin su yi yajin aiki. A wata takarda da ya mikawa kafofin labarai Suleiman Abba ya gargadi 'yansandan da su bi dokoki sau da kafa su kuma dukufa da yin aikinsu. Yace duk wanda yayi taurin kai zai gamu da hukuncin doka. Ya ce hukumar 'yansanda zata cigaba da kyautatawa 'yansandan wajen karin girma da alawus. Amma ba zata lamunci kangarewa ba.
Amma Buba Galadima yace akwai wata kullallaiya a cikin gargadin. Yace kada wani yace wai domin 'yansanda sun ce yajin aiki ba za'a yi zabe ba. Wannan tamkar yaudara ce. 'Yansandan na iya shiga yajin aiki da sanin manyansu daga bisani a ce ba za'a yi zabe ba. Yace dole za'a yi zaben ko ana so ko ba'a so.
To saidai wani dan PDP Ahmad Tandos na ganin taka tsantsan 'yan siyasa ya zama wajibi. Yace masu tada jijiyoyin wuya na shakka zabe ne domin cin bulus a neman gwamnatin rikon kwarya. Kamata yayi a fito a yi zaben kuma duk wanda yaci a bashi.
To saidai jami'an tsaro sun ce sai an samu amincewarsu ne kawai za'a iya gudanar da zaben.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.