APC Ta Tsaida Ranar Zabukan Fitar Da 'Yan Takara A Yayin Da Ta Tsawaita Wa'adin Kwamitin Rikon Kwarya

  • Murtala Sanyinna
Shugaba Buhari a wani taron gangami na jam'iyyarsa ta APC (Hoto: Instagram)

Shugaba Buhari a wani taron gangami na jam'iyyarsa ta APC (Hoto: Instagram)

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsaida ranar soma zabukan shugabannin jam’iyyar da kuma na fidda ‘yan takarar ta, a yayin da aka tunkari babban zaben kasar na shekarar 2023.

Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar ta APC na kasa John James Akpanudoedehe ya fitar, ta bayyana cewa zabukan fitar da ‘yan takarar jam’iyyar za su soma ne da tarukan zaben shugabannin jam’iyyar na matakin mazabu a ranar 24 ga watan Yulin wannan shekara.

Sanarwar ta ce tarukan zaben shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi zai biyo baya a ranar 14 ga watan Agusta, yayin da kuma za’a gudanar da na matakin jihohi a ranar 18 ga watan Satumba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kara wa’adin mulkin kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe Mai mala Buni.

Gwamna Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni

Karin bayani akan: APC, jihar Yobe, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Wannan ne kuma karo na biyu da ake kara tsawaita wa’adin na shugabannin jam'iyyar na rikon kwarya, wadanda aka nada a ranar 25 ga watan Yunin shekarar 2020, biyo bayan hukuncin kotu da ya cire Comrade Adams Oshiomhole a zaman shugaban jam’iyyar.

Da farko an baiwa kwamitin na riko wa’adin watanni 6 domin daidaita al’amuran jam’iyyar, da suka hada da sasanta bangarorin da ke takaddama, shirya babban taron jam’iyyar da kuma zaben shugabannin ta na dindindin.

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

To sai dai kuma bayan karewar wa’adin na watanni 6, an kuma tsawaita mulkin na kwamitin na rikon kwarya da wasu karin watanni 6 a watan Disamban bara, bayan da kwamitin ya gabatar da rahoton akan ayukan da ya gudanar ga Shugaba Muhammadu Buhari.