Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiyuwar Tsawaita Jagorancin Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC


Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci.
Shugaba Buhari A Taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci.

Majiyoyi daga manyan jiga-jigan jam’iyyar dai sun bayyana cewa, akwai yiyuwar a sake tsawaita jagorancin kwamitin rikon da gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta da karin watanni 6 a mako mai zuwa.

Masana a fannin siyasa sun bayyana cewa akwai saura rina a kabar a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, duba da yadda ta ke kara fadawa cikin tsaka mai wuya game da shiyoyin da ya kamata ragamar jagorancin jam’iyyar ya koma gabanin babban zaben shekarar 2023.

Majiyoyi daga cikin gida na jam’iyyar sun ce yanayin tsaka mai wuya da jam’iyyar ke ciki, ya haddasa jinkiri wajen shirya babban taron jam'iyyar, inda ya kamata a zabi shugabannin jam'iyyar kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

Idan ana iya tunawa an kafa kwamitin rikon kwarya da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ke jagoranta biyo bayan rushe shugabancin jam'iyyar a karkashin jagorancin kwamared Adams Oshiomole a watan Yunin shekarar 2020 da ta gabata inda aka tsawaita jagorancin sabon kwamitin rikon da watannin 6 a karshen shekarar ta 2020.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

Majiyoyi daga manyan jiga-jigan jam’iyyar dai sun bayyana cewa, akwai yiyuwar a sake tsawaita jagorancin kwamitin rikon da gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta da karin watanni 6 a mako mai zuwa.

Tun ba yau ba ake ta kai-komo kan bangaren kasar da ya kamata ya fitar da shugaban jam’iyyar na kasa, inda wasu ke ganincewa idan shiyyar Arewa ta samar da shugaban jam’iyyar, shiyyar kudu ya kamata ta samu tikitin dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ko kuma akasin haka.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan yanayin ya sa bangarori daban-daban na jam’iyyar ke ta zirga-zirga wajen samar da shugaban jam'iyyar na kasa, lamarin da ake alakantawa da daya daga cikin abubuwan da ke kawo jinkiri a shirin gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.

Jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da wani gwamna ma sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa, idan har ba’a tafiyar da tsarin shiyya-shiyya na jam'iyyar yadda ya kamata ba gabanin babban zaben shekarar 2023, hakan kan iya kawo rarrabuwar kai a jam'iyyar.

Wasu mambobin jam’iyyar ta APC dai sun dora laifin jinkirin da ake samu a shirya babban taron jam’iyyar kan gwamnonin jam’iyyar saboda su ne mafi karfi a jam’iyyar inda ake zargin gwamnonin da kulle-kulle a tsarin tafiyar da jam’iyyar domin samun kujerar a cewar wasu rahotanni.

Adams Oshiomohle
Adams Oshiomohle

Idan ana iya tunawa, a cikin yan kwanakin baya-bayan nan, a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, mai shari’a Taiwo Taiwo ya zartar da hukuncin yin watsi da kararraki biyu da aka shigar na neman kalubalantar rushe tsohon kwamitin da tsohon shugaban jam’iyyar ta APC, Kwamared Adams Oshiomole ya jagoranta tare da neman a rusa kwamitin riko da gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta.

Haka kuma, a cikin makon jiya ne gwamnonin jam’iyyar APC suka kada kuri’ar amincewa da salon jagorancin kwamitin rikon na Mai Mala Buni, matakin da wasu masana siyasa ke ganin na share fage ne ga wani tsawaita wa’adin da za a yi musu nan ba da jimawa ba.

XS
SM
MD
LG