Fitaccen Jarumi kuma mawaki a masana’antar Kannywood, Adam A. Zango ya gana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Ganawar na zuwa ne bayan da Zango ya sake komawa jam’iyyar APC a kwanan nan.
A shekarar 2019 Zango ya koma jam’iyyar PDP, inda ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar gabanin zabe.
Sai dai kusan makonni biyu, jarumin na Gwaska ya koma gidan da ya fito.
“Da wannan babban kifi yana cikin korama amma yanzu wannan babban kifi ya shigo cikin teku.” Ganduje ya ce a lokacin da Zango ya kai masa ziyarar.
“Yanzu zai yi ta walwala ba tare da ya bugi bango jikinsa ya kuje ba.” Gwamnan na Kano ya kara da cewa.
A kwanan nan ma an ga jarumin ya wallafa hotonsa da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni wanda shi ke rike da shugabancin jam’iyyar ta APC dake mulki a Najeriya.
A shekarun baya, ba kasafai ake ganin jaruman na Kannywood suna fitowa su nuna alkibilarsu a siyasance ba, amma a baya-baya nan lamarin ya sauya.
Akan gan su sun yi kwamba suna kai wa manyan ‘yan siyasa da sauran masu rike da madafun iko ziyara, su kuma hada kai su yi masu wakoki daban-daban.
Shigar ‘yan masana’antar ta Kannywood harkokin siyasa a cewar wasu, kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninsu, lamarin da suke yawan musantawa.