Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Haifar Da Matsalar Karancin Tsintsiya A Jihar Cross River


Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar ta Cross Rivers (Facebook/ Benedict Ayade)
Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar ta Cross Rivers (Facebook/ Benedict Ayade)

Tsintsiya ita ce alama ko tambarin jam’iyyar APC wacce ta karbi mulkin Najeriya a shekarar 2015.

Rahotanni daga jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya na cewa ana fuskantar matsalar karancin Tsintsiya a jihar.

Hakan ya biyo bayan komawar Gwamna Ben Ayade jam’iyyar APC mai mulki a watan da ya gabata, lamarin da ya sa magoya bayan gwamnan suka yi ta tururuwar sayen tsintiyar, har ta kai ga ta yanke a kasuwa.

Sai dai wata sanarwa da Sakataren yada labaran jama’iyyar, Bassey Ita ya fitar, ta ce gamnatin jihar ta yi odar tsintsiyar har miliyan 3 kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

“Domin magance wannan kalubale, jam’iyyar ta ba da odar a sayo kullin tsintsiya miliyan 3.” Sanawar ta Ita ta ce.

“Ba sabon labari ba ne cewa, juyin-juya halin tsintsiya ya fado wannan jiha ta mu, bayan da gwamnanmu ya koma jam’iyyar.”

Shugaba Buhari (hagu) Gwamna Ben Ayade (dama) (Facebook/Ben Ayade)
Shugaba Buhari (hagu) Gwamna Ben Ayade (dama) (Facebook/Ben Ayade)

Tsintsiya ita ce alama ko tambarin jam’iyyar APC wacce ta karbi mulkin Najeriya a shekarar 2015.

Sakataren yada labaran ya kara da cewa, “a makon da ya gabata, shugabannin kananan hukumomi, kansiloli, ‘yan majalisar tarayya da na jiha tare da magoya bayansu dubu 100 daga kananan hukumomin Bekwarra, Ikom da Etung suka koma jam’iyyar ta APC.”

“Abin da yanzu ya zama labari shi ne, matsalar karancin tsintsiya ta shigo jihar Cross River saboda miliyoyin mutanenmu da ke ci gaba da shiga jam’iyyar,” kamar yadda ita ma jaridar Punch ta ruwaito Sakataren yada labaran yana cewa.

XS
SM
MD
LG