Ta ce ta na da maganin matsalolin da ke damun yankin kamar dai yadda dan-takarar shugaban kasa na Jam'iyyar, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shedawa magoya bayansa a jahar Kaduna.
Ya ce “Da yardar Allah duk masu ta da hankali, da masu satar mutane, ina baku tabbaci za mu kawo karshen su.”
Shi ma dai dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ta APC, Sanata Kashim Shatima, ya ce jam'iyyar na da tsarin fidda Najeriya daga halin da ta ke ciki yanzu.
Ya ce sun ji dadin ganin addadin al'umar da suka halarci taron kuma ba za su ba su kunya ba.
Sanata Abdullahi Adamu shine shugaban Jam'iyyar APC na kasa kuma ya ce kuri'ar yankin Arewa maso yammacin Najeriya ita ce 'yar manuniyar wadda zai lashe zabe. Shugaban APC ya ce tun da Jam'iyyar ta sami karbuwa a yankin, to ta sa ran lashe zabe.
Kafin taron kaddamar da yakin neman zaben dai, sai da tawagar Sanata Bola Ahmed Tinubu ta ziyararci fadar Mai-martaba Sarkin Birnin Gwari inda gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya ce dan-takarar shugaban kasa ne da kan shi.
Ya ce an je yankin Birnin Gwarin don yi musu jajen hare-haren 'yan-bindigan da ke addabar su.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5