Sanarwar mai dauke da sa hannun Felix Morka, Sakataren Yada Labarai na Kasa, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira a matsayin “Furucin yanke kauna” da jam’iyyun adawa ke yi na nuna gwamnatin da APC ke jagoranta ba ta da wani tasiri.
A cewar sanarwar, zanga-zangar ta barke a garuruwan Minna da Kano a ranar Litinin din da ta gabata, wanda hakan ya zama shaida ta zahiri na makircin da ake zargin jam’iyyun adawa da shiryawa.
A cikin zargin, Jam’iyyar APC ta yi ikirarin cewa wadannan zanga-zangar wani yunkuri ne na ‘yan adawa da nufin haifar da tarzoma da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar kasa.
“Yayin da muka amince da ‘yancin da ‘yan kasa ke da shi na yin zanga-zangar lumana, muna kira ga mutanenmu nagari da su yi taka-tsantsan, kada su ba da kansu ga ha’incin da ‘yan adawa ke yi na yunkurin tada rigingimun al’umma ta hanyar kalamai masu tada hankali da makircinsu na yaudara" inji sanarwar.
Haka zalika, sanarwar ta jaddada kudirin gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da muhimman sauye-sauyen da suka wajaba don farfado da tattalin arzikin Najeriya da ci gaba mai dorewa.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da makirci da yunkurin rashin kishin kasa da ‘yan adawa ke yi na hargitsa kasar domin samun gindin zama nasu da kuma manufofinsu na siyasa,” in ji sanarwar.
Zarge-zargen da jam’iyyar APC ta yi na kara nuna damuwa game da yanayin siyasar Najeriya da kuma yadda za a iya ruruta wutar rikici tsakanin jam’iyya mai mulki da ‘yan adawa.
Yayin da kasar ke fama da kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da suka hada da hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi, zaman lafiyar siyasa ya kasance mafi muhimmanci ga ci gaba.
A yayin da lamarin ke faruwa, masu lura da al’amura za su sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa domin tantance tasirin da ke tattare da yanayin siyasar Najeriya da kuma yadda hakan ke haifar da tasirin shugabanci da zaman lafiya.
~Yusuf Aminu Yusuf