APC ba Zata Amince da Duk Wani Kuduri Daga Fadar Gwamnati ba

APC

Jam'iyyar APC ta umurci 'ya'yanta dake cikin majalisun dokokin Najeriya cewa daga yanzu kada su goyi bayan duk wani kuduri da ya fito daga fadar gwamnatin tarayya har sai ta warware matsalar jihar Rivers.
Jam'iyyar APC ta baiwa 'ya'yanta dake majalisun tarayya oda cewa kada su kuskura su goyi bayan duk wani kuduri da fadar gwamnatin tarayya ta gabatar masu har sai ta dauki matakan da suka dace a jihar Rivers.

Mai magana da yawun jam'iyyar ya tabbatar cewa lalle jam'iyya ta bada oda kada ma su duba duk wani kuduri da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan zata gabatar ma majalisun dokoki, wato majalisar wakilai da ta dattawa. Yanzu dai a gaban majalisar akwai batun kasafin kudi da na sabbin ministoci da shugaban kasa ya gabatarwa majalisun . Akwai kuma batun tantancewa da tabbatar da sabbin hafsan hafsoshi da shugaban kasa ya bada sunayensu. Duk wadannan ba zasu samu goyon bayan 'ya'yan jam'iyyar APC ba har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta kawo karshen rikicin jihar Rivers.

Jam'iyyar na son a kawo karshen rashin bin doka da oda a jihar ta Rivers. Ta ce ba zata yadda da irin cin tuwo da ake yiwa 'ya'yan jam'iyyarta a jihar Rivers ba. Dalili ke nan da jam'iyyar ta dauki wannan matakin. Matakin da jam'iyyar ta dauka ba wai tana son ta gwada karfinta ba ne a majalisa in ji mai magana da yawunta. Ta ce shugaban kasa ya rantse ya yi aiki da kundun tsarin milkin kasa amma kuma gashi duk abubuwan da ake yi a jihar Rivers sun saba ma dokar kasa. Saboda haka dole a dauki mataki. Matakin kuwa shi ne kin goyon bayan duk wani kuduri daga fadar gwamnati.

Kafin jam'iyyar ta janye wannan barazanar sai gwamnan jihar Rivers tare da 'yan jam'iyyar APC sun samu walwala.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

APC ba Zata Amince da Duk Wani Kuduri Daga Fadar Gwamnati ba - 2:28