Tun kafin abubuwa su baci dattawan arewa suke ta ganawa da shugaban kasa a kungiyance akai akai domin a shawo kan abubuwan da suka dami kungiyar ta arewa. Inji Farfasa Ango Abdullahi tun watan Mayun shekarar 2012 suka fara saduwa da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan a kan abubuwan dake faruwa a kasar.
Dattawan sun baiwa shugaban Najeriya abubuwan dake damunsu a rubuce, kamar abubuwan da suka baci kuma da wadanda suke baci musamman sun dauki fuska biyu a rahoton da suka baiwa shugaban kasa. Ta fuskar siyasa sun lura da abubuwan da suke tabarbarewa inda 'yan siyasa kila su jefa kasar cikin wani hali da bata tsammani. A kan halin tsaro dattawan suna gani ya kamata a sake sallo game da yadda za'a shawo kan tashin tashina da a keyi.
A cikin rahotonsu na farko kan tsaro sun jawo hankalin gwamnati kan rashin daukan matakan da zasu gano musabbabin asalin tashin hankalin domin sai an san asalin abu kana a san yadda za'a yi maganinsa. Sun fadawa shugaban cewa karfin soja ba zai kai ga nasara ba duk da shawarwarin da wasu ke ba gwamnatin ta nace da yin anfani da karfin soja. Sun nunawa shugaban kasa cewa kasa da ta fi kowace kasa karfi a duniya ta gwada yin anfani da karfin soja kuma ta kasa a kasashe da dama.
Bugu da kari dattawan sun lura cewa dakarun tsaro suna anfani da karfi da ya wuce kima da doka. Saboda haka sun bada shawara a ja hankalinsu su daina domin mutanen da suka je su taimaka idan ba sun kawo masu gudummawa ba ba zasu ci nasara ba. Idan sojoji sun je su nuna karfi ba zasu nemi hadin kan mutane ba. Duk wadannan abubuwan suka fadawa shugaban kasa a rahoton da suka bashi.
Da suka bada rahoton suna tsammani za'a sake salo domin da an yi haka da yadda ake kashe mutane kamar kiyashi da bai faru ba. A lokacin, dattawan basu san sojojin zasu yi barnar da har zata sa su kai maganar a gaban kotun kasa da kasa. Da lamarin ya kara tabarbarewa ana cigaba da kashe mutane kamar kiyashi suka dauki shawarar kai maganar gaba.
Farfasa Ango Abdullahi ya ce ba gaskiya ba ne a ce sai da hafsan sojojin Najeriya Ihejirika ya sauka suka yi barazanar kai kara. Tun yana kan kujerarsa suka sanarda yin hakan. Sabo da haka ko an saukar da shi ko ba'a saukar da shi ba abu ne da zasu kai gaba.
Ga cikakken bayani