APC Ba Ta Yi Adalci Ba Idan Ta Ki Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Kudu – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka inda ya ce sabanin hakan zai iya haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce akwai yarjejeniya da aka a jam’iyyar APC mai mulki na mika mulka ga kudu idan shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka inda ya ce sabanin hakan zai iya haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya.

“Mu dai mun sani jam’iyyar APC misali, yanzu za ta yi shekara takwas, bisa ga ka’ida da yarjejeniya da zamantakewa, ba su da zabi illa su kai shugaban kasa kudu, kuma rashin hakan, na tabbata ba zai taimakawa jam’iyyar ba kuma ba zai taimakawa ita kanta harkokin dimokradiyya ba.” In ji Kwankwaso.

Sanata Kwankwaso ya kuma sha alwashin mayar da hankali kan farfado da ilimi, tsarin kwion lafiya, bunkasa tattalin arziki idan aka zabe shi a matsayın shugaban Najeriya a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa kwakwaso ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen farfado da fannin ilimi, inganta tsarin kiwon lafiya, bunkasa tattalin arziki ta hanyar gyara bangaren sufurin jiragen sama, samar da guraben aikin yi ba tare da karbo rance daga kasashen waje ba idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

A cewarsa, APC mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta PDP sun gaza kuma kamata ya yi ‘yan kasar su duba sauya jam'iyya ta NNPP don kai su ga gaci.

A cewar Kwankwaso ba wa yaran marasa karfi ingantaccen ilimi zai rage matsalolin da ake fuskanta a Najeriya.

Baya ga bangaren ilimi, sufurin jiragen sama da kiwon lafiya, Kwankwaso ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata mayar da hankali kan arzikin da kasar ke da shi wajen gina ta a maimakon zuwa kasashen waje ciyo bashi da jikokinsa zasu rika biya nan gaba sakamakon rashin kishin wasu shuwagabanni.

Saurari cikakkiyar hirar:

Your browser doesn’t support HTML5

APC Ba Ta Yi Adalci Ba Idan Ta Ki Fitar Da Dantakarar Shugaban Kasa Daga Kudu – Kwankwaso - 3'31"