Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Wane Irin Tasiri Kalaman Kwankwaso Za Su Yi Akan Zaben 2023?


Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wasu kalamai da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi dangane da raba filaye da gwamnatin APC mai ci take yi, sun sa masu sharhi shiga yin lissafin abin da ka iya faruwa a zaben 2023.

“Za mu rushe duk wani gini da aka gina a filin gwamnati da aka mallakawa daidaikun mutane ko tsayinsa ya kai hawa dubu idan muka dawo gwamnati a shekara ta 2023 kuma mutanen Kano ilimi suke bukata ba ga daba.”

Wasu daga cikin kalaman tsohon gwamnan Kano kenan Rabiu Musa Kwankwaso a makon jiya yayin hira da daya cikin kafofin labarai na ketare (amma ba Muryar Amurka ba) da ke yada shirye-shirye da harshen Hausa.

Gabanin kalaman na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma tsohon mai magana da yawun dan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2019, Abba Kabir Yusuf wato Sanusi Bature Dawakin Tofa, a shafinsa na Facebook ya wallafa irin wadannan kalamai da ma kari akan na tsohon gwamnan.

Karin bayani akan: Rabiu Musa Kwankwaso, jihar Kano, APC, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Za mu dawo da Malam Muhammadu Sanusi na biyu karagar sarautar Kano kuma mu rushe masauratun nan na karkara da aka yi guda hudu, bayan mun sauke Sarkin Badala, mu rushe masarautun karkara kana mu rushe gine-ginen da aka yi akan filayen gwamnati- ko da sun kai hawa dubu-wadanda aka mallakawa daidaikun mutane cikin kwana 100 na farko na gwamnatin mu.”

Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida)
Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida)

Wadannnan kalamai da suka fito daga bakin madugun kungiyar kwankwasiyya a Jam’iyyar PDP ta jihar Kano da tsohon kakaki ga mutumin da ya yi wa Jam’iyyar takarar gwamna a zaben 2019 sun yamutsa hazo a fagen siyasar Kano a ‘yan kwanakin nan, inda masu sharhi kan lamuran siyasa da dimokaradiyya da ‘yan jarida da kuma wadanda suka lakanci hikima da dabarun sana’ar hulda da jama’a da yada labaru kana da ‘yan siyasa da sauran jama’ar gari, ke ci gaba da bayyana ra’ayin su.

Yayin da wasu ke ganin wadannan kalamai sun yi tsauri wasu kuwa na da fahimtar cewa, kalaman tsohon gwammnan na Kano da ma wadanda tsohon kakakin dan takarar ta PDP ya wallafa na kan tafarkin dai-dai domin kuwa hakan na daya daga cikin ginshikan da aka girka dimokaradiyya akan su wato batun fadin albarkacin baki ko kuma bayyanawa jama’a manufofi da tsare-tsare da kuma akidun jam’iyya da dan takarar ta domin samun kuri’arsu dan zabe.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Jam’iyyar APC mai mulkin Kano ta mayar da martani, tana mai bayyana cewa, burin ruguza gine-gine da kungiyar Kwankwasiyya ke alwashin idan ta samu gwamnati, takidi ne na yin barna tana mai cewa, al’umar Kano ba za su amince da barna ba.

Hon. Ibrahim Zakari Sarina da ke zaman Sakataren Jam’iyyar a jihar Kano ya ce “babu wata gwamnati da ba ta raba Fulotai (filaye) – hatta gwamnatin Soja, don haka burin rusa gine-gine a filayen da gwamnatin mu ta bayar hassadace ga arzikin da mutane suka samu”

Dangane da masarauta kuwa, Sakataren na APC a jihar Kano na cewa, masarautu sun zauna da gindinsu kuma suna nan daram, amma idan mutum na musu… “ kamata ya yi masu takidin rusa sabbin masarautun su je Rano ko Karaye ko Bichi ko kuma Gaya su ce za su rusa”

Anas Abba Dala, dan Jam’iyyar APC ne a jihar Kano wanda ke da alaka mai kyau da wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyar PDP a ciki da wajen jihar Kano ya yi tsokaci ga kalaman madugun Kwankwasiyyar na Kano.

“Na yarda da hamayya domin hamayya ko adawa ita ce ginshirin tafiyar dimokaradiyya a ko’ina a duniya, amma kalamai irin wadannan da sunan adawa na iya maryar da hannun agogo baya ga lissafin siyasar wanda ya furta su”.

Ya ce ita siyasa ‘yar lissafi ce, kuma koma nata nada lokaci, don haka lokacin yin kalamai irin wadannan ga dan siyasa bai yi ba, saboda lokacin hawa mumbarin kamfe bai zo ba.

A cewa Malam Abbas Yusha’u Yusuf, wani dan jarida a Kano, a tsari na hulda da jama’a ikirarin da kakakin Kwankwasiyya yayi na rusa duk abunda gwamnatin APC tayi da zasu ruguza su idan suka karbi mulki yayi wuri saboda a yanzu saura shekara biyu a gudanar da zaben kasa na shekarar 2023.

“Maganganu irin wadannan ka iya sa zaben 2023 a jihar Kano ya kasance ko a mutu ko a yi rai, kuma hakan ka iya sawa jam’iyyun PDP da na APC su tsayar da ‘yan takarar da ba su cancanta su mulki Jihar Kano ba”.

“Ina ganin idan haka ta faru jama’ar jihar Kano kusan miliyan 20 su ne za su cutu, saboda maimakon a samar da shugabanci nagari, za’a buge ne da samun gwamnan da zai rinka aiwatar da manufofin wasu ‘yan tsiraru”

Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)
Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)

Ko da yake, sa’o’i kalilan bayan wallafa wadannan bayanai a shafin Facebook na tsohon kakakin dan takarar gwamnnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi dan takarar Engr Abba Kabiru Yusuf ya fitar wata sanawar ta kafofin labarai musamman na intanet, inda ya nesanta kansa da kalaman yana mai cewa, kalaman ra’ayin kashin kai ne na tsohon kakakin nasa.

Sai dai furucin tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso a kafar labarai kwana daya bayan wallafa kalaman Sanusi ya jefa shakku a zukatan wasu game da sahihancin ma’anar nesanta kai da tsohon dan takara ya yi, la’akari da cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne mai gidan dantakarar da tsohon kakakin nasa.

Dr Sule Ya’u Sule na koyarwa a tsangayar nazarin aikin jarida da sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano kuma ya kware a fannin hikima da fasahar hulda da Jama’a, ya ce wannan aiki na hulda da jama’a cike yake da sarkakiya, musamman ga sha’anin siyasa da shugabanci.

A don haka, ana bukatar kwarewa da gogewa da kuma nutsuwa tare da aiki da ilimi kamar yadda ya kamata.

“A bisa ka’ida idan kana aikin hulda da jama’a ko kuma aka nada ka a matsayin mai magana da yawun ma’aikatar gwamnati, kamfani ko cibiya mai zaman kanta, hukumomin gwamnati ko jam’iyyun siyasa ko kuma kakakin daidaikun mutane, to babu shakka kai ba ka da ra’ayin kanka, ko da kuwa kana da ra’ayin to ka rasa yanayi na ‘yancin bayyana shi.

Kullum abin da za ka hada alaka da ra’ayi ko akidar shugaban ka kuma duk sanda za ka yi furuci, tamkar shi ne ya yi”

Dr. Sule Ya’u ya ce, a wasu lokutan shugabanni na amfani da masu magana da yawunsu domin gwaji ko auna mizanin martanin mutane akan wasu kalamai ko batutuwa da nufin cimma wata manufa.

Hanyar da ake gane irin wannan yanayi shi ne, a duk lokacin da irin haka ta faru, al’amarin ya gaza samun karbuwa a wurin jama’a kuma ka ji shiru babu labarin daukar matakin ladaftarwa akan shi kakakin da ya fitar da kalaman, to hakan na alamanta cewa, da masaniyar shugabanninsa.

Masu kula da lamura na ganin cewa, ko babu komai daga wadannan kalamai al’umar jihar Kano na iya fahimtar yadda wani bangare na manufofi da kudirce-kudircen gwamnatin Kano idan tsagin Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP a jihar ya samu zarafin kafa gwamnatin a shekara ta 2023.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG